'Yan sanda suka kama shi ne a wani wurin gangami da ya shirya a jajibirin shiga sabuwar shekara.
Masu fafutuka a wurin taron sun yi kokarin hana kama shi yayin da ‘yan sanda suka isa wurin gangamin a Abuja a cikin motoci bakwai kana suka kama Sowore da wasu mutane da dama ta hanyar da bai dace ba.
‘Yan sanda basu ce komai ba game da kama dan rajin da ya janyo musu suka daga kungiyoyin rajin kare hakkin bil Adama.
Ariyo Dare dake aiki da wata kungiya ta Center for Liberty Nigeria, ya ce afkawa masu bayyana ra’ayin su, ba hanya ce da ta dace a shiga sabuwar sekara da ita bane.
Wata kuma kungiya rajin kare hakkin bil Adama ta SERAP atalaice ta bada wa’adin sa’o’I 48 a sako Sowore da aka kama a ranar Juma’a in ko kuma ta kai gwamnati kotu.
Sowore tsohon dan takarar shugaban kasa ne kuma shugaban wata kungiyar juyin juya hali ta Revolution Now, wata kungiyar siyasa dake kara girma wacce take caccakar mulki mara kyau.
An kama shi a cikin watan Agustan shekarar 2019 kana aka tsare shi saboda kira da yake yi ga juyin juya hali a Najeriya. Hukumomi sun zarge shi da aikata laifin cin amanar kasa a kan gwamnati kana ana sa ido sosai a kan sa tun da aka sake a cikin watan Disamban 2019.