Aminu Saidu Dakata daga kungiyar CETAT yace sun yi taron ne da manema labarai domin su yi kira ga Shugaban kasa Muhammad Buhari ya sake duba kwamitin da ya kafa wanda Janar T. Y. Dajuma ke jagoranta.
Aikin kwamitin ne ya farfado da yankin arewa maso gabas ta duk fannonin rayuwar al'umma. Kawo yanzu Aminu Dakata yace su basa ganin aikin da kwamitin din ke yi.Wai har yanzu kwamitin bai yi wani aikin a zo a gani ba. Ko kafa jadawalin ayyukan da zasu yi sun kasa zama su yi.
Malam Ibrahim Yususf wakilin kungiyoyi masu zaman kansu na jihar Gombe yace gwamnatin jihar ta Gombe ta gudanar da wasu gine gine amma babu sauran kayan zaman rayuwa. Wuraren da aka sake gina gidajen mutane a Bauchi da Borno babu makarantu. Babu asibitoci. Babu ofishin 'yansanda da dai sauransu. Hatta kasuwa babu. Idan mutane suka koma zaman ba zai yiwu ba sai da abubuwan more rayuwa.Kwamitin na yin takatsantsan a wasu wuraren.
Amma inji ta bakin sakataren kwamitin Alhaji Tijjani Kamsa yace kwamitin ya fara gudanar da ayyuka. Kwamitin ya gina asibitoci ishirin. Ya shiga tallafawa mata da suka rasa mazajensu a jihohi uku. Kwamitin na tallafawa dalibai a makarantu. To saidai kwamitin yana gudun fara aiki a wasu wurare saboda yiyuwar 'yan ta'adan su kai hari su sake tarwatsa mutane.
Ga karin bayani.