,Gwamnati Najeriya tace bazata baiwa matasa da suka kamala karatun jami’a Naira 5000 kowane ba Gwamnati tace dama marasa galihu ne tace zata baiwa alawus alawus.
A sanarwar da fadar shugaban kasa ta bayar tace ‘yan Najeriya da dama basu fahimce ta ba kuma tun farko tayi alkawarin bada wannan kudi ne ga marasa galihu dake gararamba a cikin kasa.
Wani jigo a jami’yyar APC, Alhaji Abdu Abuja, yace wannan niyyar mai kyau da APC, ke da shi mutane ne ke masa wata fasara ta daban kuma mutane basu fahimci abunda ake nufi ba.
Ya kara da cewa wannan tsari wasu kasashe suna cin gajiyar shi a yanzu haka shine abunda ake kira “ Social Security” kuma Gwamnati na da shirin aiwatar da wannan shirin amma abun yazo a cikin mawuyacin lokaci na rashin kudi saboda halin da Najeriya ta shiga na faduwar darajar farashin Mai. Yana mai cewa wanna ba alkawarin shugaba Muhammad Buhari bane alkawari ne na party.
Tun ba yau bane masana tattalin arziki ke ganin cewa abin da kamar wuya Gwamnati ta iya cika wanna alkawari masamman idan aka yi la’akari da karyewar farashin kudin Man fetur wanda Najeriya ta dogara da shi wajen samu kudaden shiga ga kuma faduwar darajar Naira.