Tun lokacin da ya rubuta wasikar cewa zai yi tafiya bisa ga tanadin kundun tsarin mulkin kasar sashe na 145 wasu 'yan kasa na cecekuce akan wai abun da ya rubuta bai nuna cewa mataimakinsa ne mukaddashinsa mai cikakken ikon shugaban kasa ba.
To amma ministan yada labarai na Najeriya Lai Muhammad ya bayyanawa manema labarai cewa babu wani dalilin da za'a dinga cecekuce akan wasikar. Yana ganin ma ana kokarin karkata hankalin jama'a ne kawai tare da nufin kawo tashin tashina domin kada gwamnati ta samu walwalar gudanar da aikinta. Yace sashe na 145 yayi fasara a kai, wato ya bayyana lokacin da mataimakin shugaba ka iya zama mukaddashin shugaba mai cikakken iko.Duk wani bayani bayan sashen na 145 bashi da wani tasiri.
Barrister Abdulhamid Muhammad masanin kundun tsarin mulki yace duk lokacin da shugaban kasa ya rubuta wasika a karkashin sashe na 145 cewa zai yi tafiya ko bashi da lafiya mataimakinsa dole ya zama shi ne yake rike da kasa kuma duk wani bayani dake cikin wasikar bashi da tasiri. Mataimakin shugaban kasa shi ne yake kan mulki har sai shugaban ya dawo.
Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.
Facebook Forum