Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ‘Yan Arewa Mazauna Kudu Sun Yi Taron Zaman Lafiya


Taron Kungiyar 'Yan Arewacin Najeriya Mazauna Kudu
Taron Kungiyar 'Yan Arewacin Najeriya Mazauna Kudu

Wata kungiyar al’ummar ‘yan arewacin Najeriya dake zaune a kudancin kasar ta gudanar da taron zaman lafiya tare da nuna rashin jin dadi game da tabarbarewar tsaro a kasa baki daya.

Taron kungiyar ‘yan Arewacin Najeriya don tabbatar da zaman lafiya a kudancin Najeriya, an shirya shi ne a dai dai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a yankunan Arewacin Najeriya.

Lamarin da ‘yan Arewa mazauna kudancin kasar ke bayyana rashin jin dadinsu game da afkuwar rikici a yankin, inda kuma suke kira ga mahukunta na kudanci da ma Arewacin kasar da gwamnatin tarayya da su tashi tsaye wajen magance al’amura dake ci gaba da saka kasar cikin halin rashin tsaro.

Alhaji Ibrahim Dinar, dake zama ‘daya daga cikin shugabannin kungiyar, ya ce manufar kungiyar shine kawo gyara ga duk al’amuran da ke damunsu da kuma ‘kasa baki ‘daya.

Taron Kungiyar 'Yan Arewacin Najeriya Mazauna Kudu
Taron Kungiyar 'Yan Arewacin Najeriya Mazauna Kudu

An dai kafa wannan kungiya ne domin yadda ake muzgunawa wasu ‘yan kasuwa dake zaune a kudu, ta hanyar kamasu a daure ba tare da aikata wani laifi ba, inda kungiyar ke zuwa tana kwatowa duk wadanda aka kama hakkinsu.

Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin daga Lagos.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG