Jakadan Amurka a Jamhuriyar Kamaru ya kai ziyara jihar Arewa Mai Nisa dake makwaftaka da Najeriya inda dakarun Kamaru ke yaki da 'yan kungiyar Boko Haram..
Ya je ne ya gani da idanunsa yadda dakarun ke gudanar da yakin saboda korafin Amnesty International da ta zargesu da cin zarafin mutane. A cewar Amnesty sojojin na wuce gona da iri.
Jakadan ya yaba wa dakarun bisa kokarin da suke yi na dakile ayyukan 'yan ta'addan. Yana mai cewa ya karfafa wa dakarun kwarin gwuiwa kan yadda suke kokarin tsare iyakokin kasarsu da tarayyar Najeriya da Chadi da kuma kasar Nijar domin kada maharan Boko Haram su dinga shiga kasar suna kashe al'ummar da basu ci basu sha ba.
Baicin ganin dakarun Jakadan na Amurka ya baiwa kungiyar kwallon kwando ta mata gudummawar kwallaye da kuma kayayyakin karatu a jihar ta Arewa Mai Nisa.
Ga rahoton Garba Awal da karin bayani.
Facebook Forum