Gwamnatin kasar Girka ta shiga mawuyacin hali bayan da babban bankin kasashen turai ya yanke shawar kin bata bashin gaggawa. Ba tare da taimako daga waje ba, ana sa ran bankunana kasar za su rasa kudaden gudanarwa nan da safiyar gobe laraba in Allah Ya kaimu, kuma ana sa ran ko an ba Girka bashin ba za ta iya biyan biliyoyin dalolin basusukan da kasashen turai suka ranta mata a cikin watan nan.
Shugabar kasar Jamus Angela Markel, da take bayani jiya litini a Paris tare da shugaban kasar Faransa Francoise Hollande, ta fadi cewa ba a kulla sabuwar yarjejeniyar neman sassucin bashin da Girka ta nema ba. Kuma ta dora nauyin akan shugabannan kasar ta Girka, akan su dauki mataki ba tare da bata lokaci ba don cimma yarjejeniyar da masu bin tabashi don ta cigaba da kasancewa cikin rukunin kasashen dake amfani da kudaden wannan yanki.
Kuri’ar da jefa a Girka ranar lahadin da ta gabata ta nuna rashin amincewa da batun tsuke bakin aljihu da kasashen turai suke nema don su biya bashin dala biliyan 250 dake kan kasar tun shekarar 2010.