Jiya Litinin kungiyar hada kan kasashen turai (EU) ta fara gudanar da shawarwari da kasar Serbia, da kuma ta ci gaba da shawarwari da Turkiyya wanda ya cije na tsawon lokaci, matakin da daga karshe zai kai ga shigar kasashen biyu cikin kungiyar mai kasshe 28 ahalin yanzu.
Wakilan kungiyar EU'n sun bude shawarwarin ne jiya Litinin kan matakai biyu cikin 35 na shawarwari da Serbia, da zasu maida hankali kan iko da tafiyar da harkokin kudi, da kuma cikakken bayani kan yunkurin kasar na dawo da huldar difilomasiyya da kasar Kosovo.
A gefe daya kuma, wakilan kungiyar EU a Brussels sun farfado da batun neman shiga kungiyar da kasar Turkiyya take nema, bayan fiyeda shekara guda, tun bayan da shugaban kungiyar tarayyar turan Jean Claude-Juncker, yace akwai bukatar kungiyar ta sake nazarin yunkurin ta neman fadadawa.
Ba'a jin akwai daya daga cikin kasashen nan biyu da zata iya kammala sharuddan shiga kungiyar cikin wani lokaci anan kusa.