A daidai lokacin da dalibai da iyayen yara ke fatan sake bude makarantu don ci gaba da karatu, sai ga kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta kasa na barazanar daukar mataki akan rashin baiwa ilimi kulawar da ta kamata da gwamnatin Najeriya ke yi.
Da alamu kungiyar malaman kwalejojin ilimi ta Najeriya, ta zare takobi ne domin tunkarar gwamnatin Najeriya don ganin an biya mata bukatunta, wanda ta ce bukatu ne masu zummar ganin an inganta ilimi a Najeriya.
Shugaban kungiyar ta kasa reshen kwalejin ilimi ta Shehu Shagari dake Sokoto, Muhammad Mansur Ibrahim ya ce baki daya gwamnati ta nuna rashin bukatar ci gaban ilimi, dalilin da ya sa kenan ba ta bashi kulawar da ta kamata.
Ya kuma kara da cewa dukkan rubuce-rubucen da ake yi na bukatar dauki don gyaran tsarin ilimi da kuma alkawuran da gwamnatin tarayya ke yi a duk lokacin da aka yi zama ba ta cikawa.
Matsalolin ilimi dake addabar kungiyoyin malaman jami’o’i da na kwaleji duk iri daya ne, wadanda ke bukatar agajin gaggawa domin farfado da darajar ilimi a fadin Najeriya.
Sai dai wasu daga cikin iyayen yaran dake fatan a sake bude makarantu domin ci gaba da koyon darasi, sun nemi a sami hanyar sasantawa tsakanin gwamnatin da kungiyar malaman.
A baya-bayan nan dai anyi ta fitar da wasu hotunan bidiyo a kafafen sada zumunta na zamani, wadanda ke nuna yadda ginin wasu makarantun sakandare suka lalace. Lamarin da masu sharshi ke ganin koyon ilimi a irin wannan yanayi ka iya samun tagarda.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Muhammad Nasir.
Facebook Forum