Maharba da 'yan kato da gora ko "Civilian JTF" na taka muhimmiyar rawa wurin yaki da 'yan kungiyar Boko Haram.
Domin sanin inda aka kwana dangane da irin gudummawar da suke bayarwa da hasarar rayuka da suke yi ya sa maharban suka kira taron manema labarai a Yola jihar Adamawa.
Na farko sun nuna muba'ayarsu ga shugabansu da umurnin da ya basu na shiga yaki da Boko Haram. Sun shiga yakin kuma kowa ya ga rawar da suka taka.
Amma duk da gudunmawar da suke bada wa maharban suna fama da wasu matsaloli.
Kwamandan maharban a faggen daga ya bayyana irin halin da suke ciki da kuma maharban da aka kashe a fafatawarsu da 'yan Boko Haram a bakin daga.
Duk da kokarin da suke yi jami'an tsaro basa barin su shiga dajin sosai sai su barsu a baya lamarin da bai yiwa maharban dadi ba.
Sun rasa yaransu a Yobe, Yola da Mubi saboda haka sun kira gwamnatin tarayya ta yi taimaka da kayan aiki.
Shi ma shugaban hadakar kungiyoyin maharban Alhaji Muhammad Usman Tola ya bukaci a tallafa masu domin kwalliya ta biya kudin sabulu. Haka ma Malam Dogo Adamu wanda yana cikin wadanda suka fafata da 'yan Boko Haram a arewacin jihar Adamawa ya bayyana irin gwagwagwar da suka yi.
Ga karin bayani.