Wata kungiyar likitocin Najeriya ta bukaci gwamnatin kasar ta samar wa mambobin kungiyar karin kayan aiki na kariya ta kuma biya su kudin aiki na yanayi mai cike da hadari kamar na jinyar wadanda suka kamu da cutar COVID-19, ko kuma za su zafafa batun yajin aikin da suka fara ranar Litinin 15 ga watan Yuni, a cewar shugaban kungiyar.
Dokta Aliyu Sokomba, shugaban kungiyar likitocin Najeriya, ya ce yanzu haka mambobin kungiyar da ke kula da wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a cibiyoyin jinyarsu za su tsaida ayyukansu sai dai in gwamnatocin tarayya da na jihohi sun biya bukatunsu a cikin makonni biyu.
Likitoci da yawa da ba a san adadinsu ba daga kungiyar mai mambobi 5,000, wadda ke wakiltar akalla kashi uku na likitocin Najeriya sun bar ayyukansu a asibitocin gwamnati.
Akalla likitoci 10 sun mutu daga cutar COVID-19, cutar da ke saurin yaɗuwa wadda coronavirus ke janyowa. Sokomba ya nuna damuwa kan cewa kimanin likitoci 200 ne suka kamu da cutar zuwa yanzu.
Facebook Forum