Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga jama'ar jihar Katsina da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, da su kara hakuri, a daidai lokacin da ya ce jami'an tsaron kasar su na kara daukar matakan shawo kan matsalar.
Wata sanarwa da kakakin fadar shugaban kasar Garba Shehu ya fitar, ta ce "Buhari ya bayar da izinin kaddamar da wani farmaki na musamman a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina da Sokoto domin dakile ayukan 'yan ta'adda." Haka kuma ya sha alwashin kara azama kan kokarin kawo karshen ta'addanci.
Sha'anin kalubalen tsaro na kara ta'azzara a jihar ta Katsina, inda a kullum ake samun rahotannin kisan jama'a ko sace su domin karbar kudin fansa, fyade da kuma sace dukiyoyin al'umma, lamarin da ya janyo zanga-zanga a wasu yankunan jihar.
To sai dai sanarwar ta yi gargadin cewa yin zaga-zanga zai iya kawo cikas ga kokarin da sojojin kasar suke yi na yaki da ta'addabci a jihar.
A kan haka shugaba Buhari ya yi kira ga katsinawa da su "ci gaba da goyon bayan rundunar soji wacce ta jima tana aikin dakile ta'addanci."
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da zanga-zanga a jihar ta Katsina bisa alhinin yawan kashe-kashen da ake yi a yankin.
Facebook Forum