Bayan da makarantu su ka shafe akalla watanni uku a garkame, gwamnatin Najeriya ta fitar da sharuda 6 yayin da ake nazarin bude su.
Karamin Ministan harkokin ilimi a kasar, Chukwuemeka Nwajiuba ne ya bayyana sharudan a birnin Abuja.
Sai dai ya jadadda cewa, ba sai makarantu sun jira izinin budewa ba kafin su fara shirye-shiryen bin wadannan sharudan.
A cikin wadannan sharudan guda shida, na farko akwai samar da wuraren wanke hannu a cikin kowacce makaranta.
Na biyu akwai samar da wuraren gwajin yanayin zafin jikin mutum a cikin makarantun.
Na uku akwai tabbatar da cewa akwai sinadaran kashe kwayoyin jikin dan adam a yawancın kofofi da kuma dakuna.
Haka kuma akwai mayar da hankali kan yanayin tsafta a cikin harabar makarantun, na karshe kuma ministan ya ce dole ne a bayar da tazara tsakanin mutane a cikin makarantun.
Ministan dai ya yi wa makarantu gargadi kan bude makarantu ba tare da izinin gwamnati ba.
A cikin makon da ya gabata ma an garkame wata makaranta a Kaduna bayan da ta bude ba tare da izinin gwamnati ba.
An dai rufe makarantun ne a duk fadin kasar bisa kokarin takaita yaduwar cutar Coronavirus wave ta addabi duniya gabadaya.
Ya zuwa yanzu dai wadanda suka kamu da cutar a Najeriyar ya kai 16,658.
Facebook Forum