Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Kaddamar Da Allurar Rigafin Ciwon Shawara


Kungiyar Lafiya ta Duniya (WHO) tare da wasu kungiyoyin gudanar da ayyukan kiwon lafiya, sun kaddamar da yin allurar rigakafin cutar ciwon shawara da ake ce ma "Yellow Fever" a Turanci, da kuma yin feshi ta jirgin sama a fadin jihar Bauchi.

Za a iya tunawa a makon da ya gabata ne aka samu rahoton bullar cutar shawara a jihar Bauchi daya kai ga rasa rayukan wasu mutane dasuka kai ziyara dajin shakatawa na Yankari dake jihar Bauchi, wanda a sanadiyar hakanne hukumar kula da lafiya ta majalisar dinkin duniya, da hadin gwiwar wasu hukumomin ayyukan lafiya suka hada karfi domin dakile cutar, dakuma hana bazuwarta.

Dokta Adamu Ibrahim Musa Ningi shi ne jami’in hukumar kula da lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya, ya yi karin haske kan shirin yakar cutar shawarar.

Cibiyar karewa daga kamuwa da cututtuka wato NCDC tayi bayanin irin rawar da za ta taka game da shirin yaki da cutar shawarar.

Dokta Isa Mai Dabino shi ne jami’in hukumar kula da lafiya a matakin farko a jihar Bauchi, ya ce akwai sauki kan batun cutar shawarar a yanzu.

Gwamnan jihar Bauchi Senata Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi ya gode wa hukumomin kiwon lafiya da su ka kawo dauki ma jihar.

Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG