Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kasashen Afirka Ta Fara Taron Koli a Kasar Habasha


Shugaban kasar jamahuriyar Benin, Thomas Yayi Boni, wanda aka ba shugabancin kungiyar kasashen Afirka
Shugaban kasar jamahuriyar Benin, Thomas Yayi Boni, wanda aka ba shugabancin kungiyar kasashen Afirka

Shugaba Yayi Boni na kasar Jamahuriyar Benin aka ba shugabancin kungiyar

Shugabannin kasashen kungiyar Afirka sun fara taron kolin kwana biyu a Addis Ababa, tare da zaben sabon shugaban kungiyar.

Shugaban kasar Jamahuriyar Benin Thomas Yayi Boni aka ba shugabancin kungiyar har zuwa shekara mai zuwa, ya maye gurbin shugaban kasar Guinea Equatorial Teodoro Obiang Nguema.

Babban magatakardan MDD Ban Ki-moon na daga cikin masu jawaban farko a sabuwar Cibiyar kungiyar ta kasashen Afirka wadda China ta gina ma ta kyauta da kudin ta.

Mr.Ban ya gayawa shugabannin kasashen kungiyar cewa lallai a yi gaskiya da adalci a zabubbukan shugaban kasa da na majalisun dokoki da kuma na kananan hukumomi 25 da ke tafe nan gaba.

Ya bukaci gwamnatocin Sudan da Sudan ta Kudu da su gaggauta warware rikicin man da suke yi a wani yankin kan iyakar su.

Haka kuma shugaban MDDr ya ce Somalia kasa ce mai rauni amma kuma ta na da faragar samun kyakkyawar makoma a shekarun da ke tafe nan gaba.

Ana kyautata cewa shugabannin kasashen kungiyar za su tattauna akan yakin kasar Somalia kuma za su duba rikicin Sudan da Sudan ta Kudu.

Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya na jawabi a wajen taron kolin kungiyar kasashen Afirka a ranar Lahadi 29 ga watan daya shekarar dubu biyu da goma sha biyu
Babban Magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon ya na jawabi a wajen taron kolin kungiyar kasashen Afirka a ranar Lahadi 29 ga watan daya shekarar dubu biyu da goma sha biyu

Ranar Asabar kungiyar kasashen Afirka ta yaye kallabin sabuwar Cibiyar ta, ta dola miliyan 200 wadda China ta gina ma ta kuma ta ba ta kyauta.

Bikin kaddamar da sabuwar Cibiyar ya samu halartar babban mai ba gwamnatin China shawara a harakokin siyasa, Jia Qinglin, da frayim ministan kasar Ethiopia Meles Zenawi da kuma sauran shugabannin kasashen Afirka.

Jia ya ce sabon ginin cibiyar kungiyar kasashen Afirkar, wata shaida ce da ke nuna abotar da ke tsakanin China da al’ummar Afirka. Haka kuma ya yabawa cinikayyar da ke bunkasa tsakanin China da kasashen Afirka.

Frayim minista Meles ya yabawa abun da ya kira farfadowar Afirka, da aka girka bisa wani tsarin da ya yi koyi da salon tattalin arzikin gwamnatin kasar China. Haka kuma ya yi amfani da damar da ya samu ya soki lamirin tsarin tattalin arzikin kasashen yammacin duniya a wannan karni, wanda ya kwatanta da neman kibar da ta tono rama.

XS
SM
MD
LG