Kungiyar ta bayyana cewa, tallafawa Marayu da Matan zai ba su damar kulawa da marayu da hakan zai hana tada kangararrun yara da kan zama 'yan ta'adda ko mashaya miyagun kwayoyi da kuma hana barace barace.
An gudanar da taron yaye matan a farkon makon nan a helkwatar JIBWIS dake Abuja inda matan su ka nuna basirar su da abubuwan da su ka koya kama daga man shafawa, man gyaran jiki, maganin sauro da sauran su.
An ware mata shida da su ka fi sauran kwazo inda a ka ba su kyautuka da yi mu su fatan su ma za su koyar da wasu matan sana'ar da hakan zai taimaka mu su wajen kula da yara marayu da ke gaban su da sauran bukatun yau da kullum.
Daya daga manyan baki a taron, Alhaji Abdullahi Abdulmalik Diggi ya ba da kyautar Naira dubu N180,000 ga mata shida mafiya kwazo.
Shugaban kwamitin Alhaji Sa'idu Musa Yelwa ya bukaci gwamnati ta rika shigowa lamarin don akwai dimbin marayu da matan da mazan su ka rasu a Abuja.
A yanzu a kan gudanar da taron sau daya a shekara, don hakan ya sa kwamitin nazarin yin taron fiye da sau daya domin yawan mabukata a cikin al’umma.
Saurari rahoton Nasiru Adamu El-hikaya cikin sauti:
Facebook Forum