Da yake damka wannan tallafi a hannun shuwagabanin rundunar mayakan sojojin jamhuriyar Nijer jami’in kula da ayyukan soja a ofishin jakadancin Amurka, Kanar Jimi Krischki ya bayyana cewa, "sananen abu ne cewa ambaliyar ruwan da aka fuskanta a bana ta matukar haddasa cikas ga rayuwar ‘yan Nijer, saboda haka ya zama wajibi mu tallafa wa jama’a a matsayinmu na abokan hulda na fannin tsaro da zaman lafiya. Muna tare da ku."
Mataimakin shugaban sashen kula da ayyukan inganta rayuwar dakarun Nijer, Kanar Dodo Boubacar ya yaba da wannan yunkuri dake zama wani matakin kare iyalan sojoji daga cututtukan dake da nasaba da ruwa. Commandant Aichatou Ousman na daga cikin jami’ai a wannan ofishi dake karkashin ma’aikatar tsaron kasa, kuma ta ce ambaliyar ruwan ta zo da cututtuka iri iri da sauran matsaloli, don haka tallafin da aka kawo zai taimaka matuka.
Matan sojojin da aka bai wa wannan tallafi, ta bakin mai magana da yawun kungiyarsu, Mme Maty Aissa Souley, sun yi hamdala.
Ba’idin kayan tsaftace jiki da na kare kai daga kamuwa da cutitika tallafin na kasar Amurka ya kumshi wasu kayan nishadi da nufin karfafa dangantaka tsakanin sojoji da fararen hula.
Ruwan saman da aka tafka a bana ya haddasa mumunar ambaliyar da ta jefa dubban ‘yan Nijer cikin mawuyacin hali cikinsu har da iyalan sojoji saboda haka bayan tallafin da ta bayar a kwanakin baya domin fararen hular da suka tsinci kansu cikin wannan iftila’i, kasar Amurka ta ga cancantar bada wani tallafin na daban domin iyalan dakarun tsaro.
Ga Souley Barma da cikakken rahoton:
Facebook Forum