An bada wannan jawabine a kan dandalin Amaqna yada labaran kungiyar yan bindigan. ISIS ta taba anfani dairin wannan ikirarin a wasu hare-haren da ta kai a can baya. Sai dai babu wani martanin gaggawa daga hukumomin Amurka a kan wannan ikirari na ISIS
Artan ya saka wasu saknoni a kan shafinsa na Facebook mintocikafin harin na ranar Litinin din shekaranjiya, inda ya zargi Amurka da laifinkashe musulmi a kasashen waje kuma ya jinjinawa shehun malamin nan na al-Qaida Anwar al-Awlaki a matsayin jarumi, kamar yanda yan sandan Amurka ke fadawa kafofin yada labarai.
Har izuwa yau dai hukumomi na kokarin gano dalilin da yasa Artan ya kai wannan harin a jami’ar dake birnin Columbus, amma kuma a bayanin da ya rubuta cikin Facebook yace yana son ya hallaka milyoyin abinda ya kira “kafirai” don ja wa Amurka burki daga “tsoma bakin” da take yi a harkokin wasu kasashe.