Kungiyar CISLAC mai sa ido a ayyukan yaki da cin hanci da rashawa ta bude wata cibiya mai suna ALAK da za ta taimaka wajen kulawa da masu kawo koke akan cin hanci da rashawa da kare yancin wadanda aka zargi da laifin cin hanci da ma wadanda aka tauye masu hakin su na dan Adam.
Shugaban Kungiyar CISLAC Auwal Musa Rafsanjani ya ce cibiyar za ta rika tattara bayanai tare da bin diddigin laifuka da suka shafi cin hanci da rashawa har a hukunta masu laifin baya ga taimakawa wajen shigar da koke koken.
Wanan Cibiya ita ce irinta ta farko a Najeriya kuma an kafa ta ne tare da hadin gwiwa da Hukumomin Yaki da Cin Hanci da rashawa ta Kasa.
Bincike ya nuna cewa Najeriya na hasarar kashi ashirin da biyar cikin dari na arzikin ta a fanin cin hanci da rashawa kuma an shigar da kararraki da yawa amma har yanzu ba a hukunta kowa ba.
Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:
Facebook Forum