Kungiyar ta sanarwa taron manema labarai ta bakin shugabanta Yerima Hazron Fada da ta kira a cibiyar ‘yan jaridu ta Najeriya reshen jihar Adamawa lokacin da kungiyar ke maida martini ga kalaman kwamishinan ‘yan sanda na ranar biyu ga watannan inda yake cewa ba a sami asarar rai ko daya ba biyo bayan harin da fulani makiyaya suka kai kauyen Kodomun na karamar hukumar Demsa kwanaki uku a jere da ya yi sanadin mutuwar mutane ashirin da biyar.
Cikin jawabin da ya karantawa ‘yan jarida, shugaban kungiyar ya yi gargadin al’umarsa za su dauki matakan tsare rayukan jama’arsu da dukiyoyinsu matukar gwamnatin jihar Adamawa da jami’an tsarro basu dauki tsauraran matakai na tsaron lafiyarsu, dukiyoyi da sake tsugunar da mutane sama da dubu biyu da dari biyar da rikici sakanin Fulani makiyaya da manoma ya raba da muhallansu ba.
Wani Hon, Garba daya daga ciki magabatan kungiyar Pene Da Bwatiye da na yi hira da shi ‘yan mintoci bayan kamala taron ‘yan jaridu da kungiyar ta kira, ya ce bukatunsu sun hada da sake tsugunar da jama’arsu, kafa kotun sauraron keta hakkin bil’adama da kuma na sifeton janar na ‘yan sandan Najeriya ya tsige kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa saboda sakaci da rashin sanin makamar aiki.
Wakilinmu Sanusi Adamu na dauke da sauran rahoton.