Bayan ganawar babban daraktan Alhaji Baru ya bayyanawa manema labaru cewa babu wani shirin kara kudin mai sabanin irin labarun da aka dinga yayatawa a kafofin labaru ta yanar gizo.
Ya sake nanatawa cewa gwamnatin Buhari bata da niyyar kara kudin farashin man fetur yanzu ko a nan gaba.
Shi ma babban sakataren 'yan kasuwa masu hada hadar man fetur Alhaji Danladi Fasali yace ko su basu da niyyar kara farashin man fetur. Yace kwai babbar alama cewa za'a rage farashin man saboda suna ta kawo kaya. Yace yanzu dai an kurewa man fetur farashi.
Alhaji Fasali yace a shirin da su keyi idan kayansu na gaba suka iso zasu sayar dasu kasa da farashen gwamnati. Ko yanzu ma akwai wasu 'yan kasuwa dake sayar da man kasa da farashen gwamnati. A Legas akwai wani kamfani dake sayarwa dari da talatin da daya maimakon dari da arba'in da biyar. Yace kudin kara sauka ya keyi ba wai yana karuwa ba ne.
Ga rahoton Umar Faruk da karin bayani.