Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Noma Shi Ne Kan Gaba A Gwamnantinmu - Shugaba Buhari


Shugaba Muhammad Buhari
Shugaba Muhammad Buhari

Shugaba Buhari yace gwamnatinsa zata cigaba da ba noma fifiko a cikin tsare-tsarensu da duk abubuwan da suka tsara na ingiza 'yan kasar domin su tanadi cimakar da zata wadatar da kasar.

Yayinda yake jawabi a wurin yiwa Mr. Hoang Ngoc Ho jakadan kasar Vietmnam bankwana a fadarsa jiya Talata, shugaba Buhari yace gwamnatinsa ta maida hankali kacokan akan harkokin noma da zummar samun isasshen abinci a kasar da farfado da tattalin arziki da kuma kirkiro ayyukan yi.

Yace "Muna nufin zaburar da 'yan Najeriya su bi akidar yin aiki tukuru dangane da noma. Zamu cigaba da yin aiki kafada da kafada da wasu kasashe da zasu taimaka wurin karkata tunanen 'yan Najeriya su rungumi noma gadan gadan. Mun yi imanin cewa habaka ayyukan noma kamar yadda kasar Vietnam tayi, musamman bayan yaki a shekarar 1975. Idan mun yi hakan zamu cigaba", inji shugaba Buhari.

Shugaba Buhari ya taya kasar Vietnam murna da zabar hanya mafi dacewa, wato noma, da tayi sanadiyar ciyar da kasar da ma duniya.

Kasarku ta cancanta a yaba mata dangane da wannan cigaba da ta samu, inji shugaba Buhari.

Daga karshe Jakada Ho ya bayyana gamsuwarsa da irin kyakyawar dangantakar dake tsakain kasarsa da Najeriya musamman a lokacinsa. Yayi misali da hadin kan dake tsakanin kasar Vietnam da wasu jihohi a harkokin noma, lamarin da yace ya dada karfafa zumunci.

Yace kasarsa ashirye take ta taka babbar rawar gani wajen farfado da tattalin arzikin kasar, musamman wajen bada goyon baya wa sabbin tsare-tsaren gwamnatin Buhari.

XS
SM
MD
LG