A wata sanarwa da ya aikawa manema labaru kakakin hedikwatar dakarun kasashen yankin tafkin Chadi Kanal Mohammed Dole, yace daruruwan mayakan Boko Haram sun ajiye makamansu suka mika kai. Kara tsawwala matakan da ake dauka akansu shine ke dalilin fitowar mayakan suna mika wuya, yanzu dai akwai mayaka 240 da suka riga suka mika wuya.
Yayin da a bangaren Chadi mayakan ke mika wuya sai gashi a bangaren Najeriya sai ‘kara kai hare hare suke yi, a cewar Mohammed Dole hakan na faruwa ne a duk lokacin da aka bude musu wuta a wani bangare sai su gudu zuwa wani bangare.
Dakta Bawa Abdullahi Wase, na ganin girman filin kasa ne ke haddasawa mayakan dake yankin tafkin Chadi mika wuya, kasancwar sojojin hadin gwiwa sun bude musu wuta babu yadda zasuyi wajen sake komawa wani bangaren.
Domin karin bayani.