Nahiyar Afirka ta ga cigaba da kuma koma baya a yaki da coronavirus. A wannan makon, jami’ai sun yi marhaban da bude cibiyar sadarwa na dakunan gwaje-gwaje masu tsara kwayar halitta.
Darektar yankin Afirka ta hukumar lafiya ta duniya WHO, Dr. Matshidiso Moeti, ta sanar jiya Alhamis cewa WHO da kuma hukumar dakile cuttuka masu yaduwa ta Afirka sun bude dakunan gwaje-gwaje 12 a nahiyar don yin aiki kan tsarin kwayar COVID-19 da kuma nazarin bayanai.
Ta ce “Wannan hanyar sadarwar za ta taimaka mana wajen bin diddigin yadda kwayar cutar take yaduwa don samar da allurar rigakafi da kuma magunguna da suka dace da mutanen Afirka. Kuma hakan zai taimaka mana ya zama mun wuce gaba a yaki da cutar COVID-19.
Sai dai kuma duk da wannan ci gaba, an samu koma baya. An dakatar da gwajin allurar rigakafin na farko, da ake yi a Afirka ta Kudu.
Babban kamfanin harhada magunguna na Birtaniya da Sweden Astra-Zeneca ya sanar a wannan makon cya dakatar da gagarumin gwaje-gwajen allurar rigakafin COVID-19 saboda wani wanda ya shiga cikin shirin a Birtaniya ya kamu da rashin lafiya bayan karbar magungunan gwajin.
Facebook Forum