Kumbon zuwa sararin Subahana na Amurka mai suna “space shuttle Discovery” ya kammala aikinsa a Tashar Sararin Sama ta Kasa da Kasa a karo na 39 na zuwansa tashar, kuma yana shirin saukowa gobe Laraba a Cibiyar nazarin sararin Subahana mai suna Kennedy Space Center da ke Florida.
Kumbon ya yi nasarar tashi daga tashar ta sararin sama tun ranar Litini da safe. Bayan kammala aikinsa na kwanaki 13, kumbon ‘Discover’ zai yi ritaya a matsayin kumbon da ya fi dadewa ya na aiki tun farkon wannan shirin cibiyar NASA yau shekaru 30.
Kumbon mai dauke da ‘yan sama jannati maza biyar da kuma mace daya sun yi kusan kwanaki tara a tashar ta sararin sama, bayan da cibiyar ta NASA ta kara kwanaki biyu ga tsawon zamansu. Baya ga jigilar kayaki ga tasoshin da ke zagaye falakai, ‘yan sama jannatin cikin Discovery din sun kuma girke wata na’urar adana abubuwa daban daban a sashen da ke fuskantar duniya na tashar sararin sama din.
Sun kuma kai wata mutum mutumiyar na’ura, mai suna Robonaut 2. NASA na fatan sannu a hankali za a iya inganta Robonaut 2 ta iya aika tamkar mai taimaka wa ‘yan sama jannati a tashar.