Ana fargabar cewa akalla daruruwan mutane sun hallaka a cikin wata gagarumar girgizar kasar da ta abkawa kasar Japan, wacce kuma ta haifarda wata girgizan ta karkashin teku da ta bakado ruwa izuwa cikin mazaunun jama’a.
Wannan mahaukaciyar girgizan kasan da akace itace mafi muni da ta taba abkuwa a Japan a cikin shekaru 100 da suka gabata, ta tapka masifar barna akan gine-gine barkattai, kuma dimbin mutane da yawa sun salwanta, ana kuma jin tsoron kila duk sun hallaka ne.
Wannan girgizan kasan, mai karfin maki 8.9, ta faru ne a wani wuri dake da tazaran km 125 daga gabar tekun japan, abinda yassa aka fara shelar janyo hankalin jama’ar wurare da dama gameda abkuwar girgizan teku da ake kura “tsunami” wacce zata iya shahuwar hatta mutanen dake zaune a nahiyar kudancin Amurka, da kuma daukacin dukkan sassan yammacin ita kanta wannan Amurka din da muke ciki.
Yanzu hakan ma waya gabjeje iyar tsunami mai tafe da giwar ruwan da tsawonta ya kai mita 10 na can tana fattatakar yankunan bkin gabar tekuna a can Japan.
Wani matashin dalibi dake karatu a birnin Tokyo ya bayyana irin tashin hankalin da suka shiga lokacinda girgizan kasar ta riske su.