Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudurin Dokar Da Zai Ba Mata Kujeru a Majalisun Dokokin Najeriya


Taron Majalisun Dokokin Najeriya.
Taron Majalisun Dokokin Najeriya.

A yanzu mata 8 ake da su a Majalisar Dattawa, sannan 13 a Majalisar Wakilai - adadin da ke nufin kashi 4.4 a cikin 100 kacal ke Majalisar.

Majalisar Dokokin Najeriya na shirin yin wata doka da za ta ba mata da ke son tsayawa takara mazabu na musamman, inda su kadai ne za su tsaya takara a wadannan mazabun.

Sai dai masu nazari a al'amuran yau da kullum na ganin ba abu ne mai yi wu ba, domin sai an yi wa dokar kasa garambawul.

Kudurin dokar wacce mataimakiyar mai tsawatarwa a Majalisar Wakilai daga Jihar Abia, Nkiru Onyejiocha ta kawo, ya samu hadin gwiwar 'yan Majalisar 100 cikihar da shugaban Majalisar Wakilan Femi Gbajabiamila.

Wannan dokar na neman a canja sashi 48 na kundin tsarin mulkin kasa da zai sa a samu kujeru hudu a Majalisar Dattawa, wato Sanatoci uku daga ko wacce Jiha kuma daya daga babban birnin taraiyya Abuja wanda za su kasance mata.

A yanzu mata 8 ake da su a Majalisar Dattawa, sannan 13 a Majalisar Wakilai wanda ya ke nufin kashi 4.4 a cikin dari ne kacal ke Majalisar.

Malami a tsangayar siyasa da diflomaciyar kasa da kasa a Jami'ar Baze, Farfesa Usman Mohammed yana ganin wanan kudurin ba mai yiwuwa ba ne domin mata sune matsalar mata yan uwan su.

Farfesa Usman ya ce mata kashi 70 ne ke zabe kuma ba sa zaben mata 'yan uwansu, kuma sukan yi gaba da juna har ba sa ga maciji. Wannan alama ce ta cewa abin ba zai yi nasara ba.

Ya kara da cewa, shi ba ya goyon bayan wannan doka domin za a ba 'yan Najeriya wahala ne kawai domin za ta bukaci a canja kundin tsarin mulki.

Ita ma Hajiya Hauwa Bukar wace ta taba rike mukamin shugabar Mata a shiyar Arewa maso Gabas, ta ce ta yi farin cikin jin wannan yunkurin da Majalisar kasa ke yi.

Hauwa Bukar ta ce su mata 'yan siyasa sun dade suna neman wannan dokar, kuma ana yi a kasashe irin su Indiya wadanda suka fi Najeriya yawan al'umma, saboda haka abu ne mai kyau Najeriya ta yi koyi da shi saboda a dama da mata.

Idan an yi dokar, mafi karancin mata a Majalisar Dattawa za su zama 37 a cikin mutane 109, sannan a Majalisar Wakilai kuma za su zama 74 a cikin yan Majalisa 360. Yanzu haka dai dokar ta shiga karatu na biyu a Majalisar Wakilai.

Domin karin bayani saurari rahotan Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:04 0:00


XS
SM
MD
LG