A sakonnin da suka aika na wanann bikin, shugabannin addinin Kirista da ma sauran shugabanni sun bukaci jama’ar kasar su rungumi zaman lafiya tare da nuna kaunar juna domin kuwa cikin darussan da ake so a dauka a bikin na Easter.
Yanzu haka ma dai tuni aka umarci jami'an tsaro a kasar, da su tabbatar da tsaro ga masu ibada da kuma matafiya har ma da sauran al’ummar Najeriya a lokacin gudanar da wannan biki wanda aka fara a yau jumma'a da Kiristoci ke kira Good Friday.
Arch Bishop Stephen Dami Mamza, shugaban Majami'ar Katolika a jihar Adamawa, wanda kuma shine shugaban kungiyar kiristocin Najeriya, CAN, reshen jihar ya bayyana muhimmancin bikin Easter.
A lokutan biki irin wannan akan samu hadaka da yan uwantaka a tsakanin mabiya addinai mabanbanta, abin da Bishop Mamza ke kiran da a farfado da shi.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Facebook Forum