Alkali Okon Victor Abang, ya rubuta umarnin dakatar da taron da yayiwa hukumar zabe da ‘yan sanda kwafin umarnin, da barazanar sanya a damke shugabannin kwamitin rikon idan har sun ki bin umarnin kotun.
Musamman sanarwar ta gargadi kalamai da ke fitowa daga ‘yan kwamitin rikon da suka hada da Ben Obi da Dayo Adeyeye, da kotun ke dauka a matsayin isgilanci. Shugaban kwamitin amintattun na PDP Sanata Walid Jibrin, ya fadawa wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu, cewa taron na nan kamar yadda aka tsara. Shi kuma kakakin bangaren Sanata Ali Modu Sheriff, Inuwa Bwala, yace taron ya sabawa doka.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na hukumar zabe Nick Dazan, ya bawa PDP shawara, inda yace “abin da yakamata ayi aje ayi sulhu, a zauna kowa ya fadi menene yake mishi zafi, saboda yawan zuwa kotu ba karamin kudi ake kashewa ba, abu na biyu, ba karamin lokaci ake kashewa ba, na uku ba karamin bacin rai zai biyo bayan kace nace da kuma zuwa kotu ba.”
Tun gabanin wannan hukuncin na Abuja, babbar kotun tarayya ta Port Harcourt ta bayar da hurumin gudanar da babban taron. Abin jira a gani shine shin taron zai gudana kamar yadda aka tsara? Shin hukumar zabe zata halarci taron?
Saurari rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.