Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Najeriya Ta Tuhumi Funke Akindele-Bello Da Laifin Karya Doka


Nigerian Actress Funke Akindele Bello
Nigerian Actress Funke Akindele Bello

Wata kotu a Najeriya ta yanke wa Funke Akindele-Bello, wata tauraruwar wasan fina-finan Nollywood hukuncin yi wa al'umma hidima bayan da ta amsa laifin karya dokar hana fita, sakamakon wani taron liyafar zagayowar ranar haihuwar mijinta da ta shirya, yayin da kuma a gefe guda ta ke yin fadakarwa akan muhimmancin yin nesa-nesa da juna a wannan lokacin na annobar cutar coronavirus.

Bayan kama ma'auratan biyiu (Funke da mijinta), sun gurfana a gaban kotu a jiya Litinin bisa tuhumar karya dokar jihar Legas, inda aka yanke musu hukuncin yin aikin hidima ga al'umma tsawon kwanaki 14 aka kuma ci su tara.

Asirin ma'auratan ya bayyana ne a ranar Asabar 4 ga watan Afrilu a lokacin da mijin tauraruwar, Abdulrasheed Bello ya sanya hoton bidiyon bikin a shafinsa na sada zumunta.

An caccaki Funke da yin watsi da matakin da ita da kanta take ba jama'a kwarin gwiwa da su bi, bayan da Najeriya ta haramta taron jama’a da ya zarta mutane 20 a jihohi uku don rage yaduwar cutar coronavirus a watan da ya gabata.

Ya zuwa yanzu, cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya ta bayyana cewa fiye da mutum 200 ne suka kamu da cutar coronavirus a kasar, kuma mutane biyar sun mutu daga cutar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG