Rundunar kasashen yankin tafkin Chadi na ci gaba da kai zafafan hare-hare a matattarar ‘yan ta'addan Boko Haram dake zirin tafkin, musamman wadanda suka fake a tsibiran wuraren.
Farmakin wanda yanzu sojojin suka canzawa salo, ana kai shi ne ta sama da ta kasa da kuma taimakon jiragen yakin sojojin saman Najeriya da Nijar, wadanda suka dauki lokaci suna barin wuta a maboyar ‘yan ta'addan.
Kakakin rundunar kawancen, Kanar Timothy Antiga, ya bayyana cewa a harin baya-baya da suka kai, an kashe kimanin mayakan Boko Haram goma sha tara tare da kwato motoci, bindigogi, harsasai da sauran miyagun makamai daga hannun mayakan.
Sojojin kawancen dake bangaren Kamaru wato “SECTOR 1” sun yi wa mayakan Boko Haram da suka tsere ta kudancin tafkin Chadin kofar rago, yayin da ta gabashin Chadi kuma aka fatattake su musamman a yankin Litri Da Madayi.
Tuni dai masana hakokin tsaro irin su Janar Junaidu Sani Bindawa suka nuna kwarin gwiwa bisa wannan sabon yunkuri na sojojin yankin tafkin Chadi. Junaidu ya ce in aka ci gaba da haka to lallai kwanan nan za a cimma muradi.
Saurari karin bayani cikin sauti.
Facebook Forum