Yayin da cibiyoyin bincike suka dukufa wajen lalubo hanyoyin dakile annobar Coronavirus, sashen koyar da kimiyyar hada sinadaran masana’antu na Jami’ar Bayero da ke Kano ya fara samar da sinadarin da ke kashe kwayoyin cuta, wanda ake yawan amfani da shi a hannu a wannan lokacin da Coronavirus ke yaduwa.
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fuskantar karanci da kuma tsadar kayayyakin kare kai daga hadarin kamuwa da cutar a Najeriya.
Dr Ibrahim Tajo Siraj da ke zaman shugaban sashen koyar da kimiyyar hada sinadaran masana’antu na Jami’ar Bayero da ke Kano ya ce a karon farko sun samar da kwalabe kimanin dubu uku domin raba wa kyauta ga al’umomin da ke Jami’ar.
Ya ce "muna aiki da NAFDAC domin tantance kayanmu sa'annan mun kirkiro wannan sinadarin ne a matsayin taimako ga jam'a ba wai don a sayar ba, kuma a ganinmu namu zai fi duk wanda ake sayarwa yanzu a kasuwa inganci."
Mutane da dama sun yi maraba da wannan matakin saboda yadda tun bayan bullar cutar Coronavirus a Najeriya kayayyakin kandagarkin kamuwa da ita suka yi tashin gwauron zabbi a kasar, baya ga karancinsu da ake fuskanta.
Saurari wannan rahoton a sauti.
Facebook Forum