Wata kotu a Birtaniya ta tuhumi tsohuwar shugabar kungiyar kasashe masu arzikin mai ta OPEC, Diezani Alison-Madueke da laifin karbar cin hanci a lokacin tana rike da mukamin ministar mai a Najeriya.
Hukumar da ke yaki da manyan laifuka ta NCA a Birtaniya ce ta bayyana hakan a ranar Talata.
“Muna zargin Diezani Alison-Madueke ta yi amfani da kujerarta a Najeriya ta karbi kyautar kudade saboda ta ba da wasu kwantiragi na miliyoyin fam,” In ji Andy Kelly da ke shugabantar sashen laifukan kasa da kasa a hukumar ta NCA.
An ba da belin Alison-Madueke mai shekaru 63 tun bayan da aka kama ta a watan Oktoba a London a shekarar 2015.
A ranar 2 ga watan Oktoba ake sa ran za ta gurfana a gaban kotu a cewar NCA.
Lauyan tsohuwar ministar man ya fadawa AFP cewa Alison-Madueke za ta kalubalanci zarge-zargen da ake mata.
Alison-Madueke ta rike mukamin ministar mai a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan daga 2010 zuwa 2015.
Ta kasance mace ta farko da ta rike mukamin ministar mai a Najeriya da mukamin shugabar kungiyar ta OPEC.
Dandalin Mu Tattauna