Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Gano Karin Dala Miliyan 72 Da Aka Alakanta Da Diezani


Tsohuwar ministar man fetur a Najeriya Diezani Alison-Madueke a birnin Houston na Amurka, a watan Maris din 2014.
Tsohuwar ministar man fetur a Najeriya Diezani Alison-Madueke a birnin Houston na Amurka, a watan Maris din 2014.

Diezani, na daya daga cikin mashahuran jami’an gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan,

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya, ta sake bankado wasu makudan kudade da ake alakantawa da tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison-Maduke.

Rahotanni sun ce an gano dala miliyan 72.8 da aka boye a wani asusu a bankin Fidelity.

Bayanai da jaridun Najeriya suka wallafa sun nuna cewa gano kudaden ya sa an kama tsohon Manajan Bankin Nnamdi Okonkwo.

Okonkwo shi ne manajan bankin na Fidelity a lokacin da Maduke ke rike da mukamin ministar man fetur.

A halin yanzu hukumar ta EFCC na tsare da Okonkwo a wani yunkuri na gano inda kudaden suke.

Alison-Maduke, na daya daga cikin mashahuran jami’an gwamnatin tsohon shugaba Goodluck Jonathan, ta kuma dade tana tserewa hukuma bisa zargin da aka mata na karkata akalar kudaden ma’aikatar man fetur da ta jagoranta.

A baya hukumar ta EFCC ta taba tsare Okonkwo tare da wasu mutane kan wasu kudade da yawansu ya kai dala miliyan 153 da kuma dala miliyan 115 kamar yadda wata sanarwa da hukumar ta EFCC ta fitar ta ce.

Hukumar ta ce tuni dai ta karbo dala miliyan 153 amma har yanzu ba kammala batun dala miliyan 115 ba saboda shari’o’i da ke gaban kotu.

XS
SM
MD
LG