Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Nijar Ta Gayyaci Jakadan Aljeriya Domin Nuna Bacin Ranta Kan Walakanta 'Yan Ci Ranin Nijar


Jakadan Aljeriya a Nijar
Jakadan Aljeriya a Nijar

Gwamnatin mulkin sojan kasar Nijar ta gayyaci jakadan kasar Aljeriya a kasar inda ta nuna masa bacin ranta kan abinda ta kira wulakancin da ‘yan Nijar masu ci rani a kasar Aljeriya ke fuskanta.

AGADEZ, NIGER - Gwamnatin Nijar dai ta bukaci jakadan kasar Aljeriya da ya yi magana da gwamnatin kasarsa domin kawo karshen cin zarafin da ‘yan Nijar ke fuskanta da ma na wasu kasashen Afirka ta yamma.

Abdourahamane Dikko masanin harkokin yau da kullun a Nijar ya bayyana gamsuwa kan matakin na mahukuntan Nijar.

Kusan kowane karshen wata kasar Aljeriya na koro ‘yan kasar Nijar dama na wasu kasashen Afirka a cikin mawuyacin hali bayan rabasu da dukiyoyinsu kamar yadda wasu ‘yan kasar ta Nijar da kasar Aljeriya ta koro a makon da ya gabata suka shaidawa Muryar Amurka.

Acewar Sulaimane Issaka, wanda jami’in gwamnati ne, ya bayyana irin halin da mahukuntan kasar Aljeriya ke kwaso ‘yan ci ranin kasar Nijar a cikin yanayi na cin zarafi.

Masana na ganin matakin gayyatar jakadan Aljeriya a Nijar bazai kawo karshen wannan matsalar ba illa kawai hukumomin su samar da hanyoyin rage talauci a tsakanin al’umma da kuma samarda ayyuka na dai dai da sauran kasashen.

Al’ummar Nijar dai sun zura ido su ga tasirin da wannan matakin zai yi na gayyatar jakadan kasar Aljeriya a Nijar wajen shawo kan wannan matsalar ta ‘yan ci ranin Nijar a kasar Aljeriya.

Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmoud:

Gwamnatin Nijar Ta Gayyaci Jakadan Aljeriya Domin Nuna Bacin Ranta Kan Walakanta 'Yan Ci Ranin Nijar .mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:20 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG