Da take yanke hukunci akan shari’a tsakanin gwamnatin Najeriya da kungiyar ASUU, Kotun masana’antu ta kasa ta tabbatar da CONUA da NAMDA a matsayin hallartattun kungiyoyin masu cin gashin kansu wadanda suka yi rajista da kungiyoyin kwadago kana suna da ‘yanci su gudanar da ayyukan su a manyan makarantun Najeriya.
ASUU ta yi karar Ministan kwadago da ayyuka, registra, kungiyoyin kwadago, CONUA da NAMDA a matsayin wadanda take tuhuma guda hudu.
Da ya ke gabatar da hukunci, mai shari’a Benedict Kanyip ya jaddada cewa bisa dokokin kungiyar kwadago ta duniya wato ILO, ya hallarta a samu kungiyoyin kwadago sama da guda a ma’aikata daya.
Mai shari’ar ya kuma kara jaddada cewa, sabanin hujjojin da mai shigar da kara ta dogara da su na sashi na uku cikin baka 2 na dokokin kungiyoyin kwadago wanda ya haramta wa wadanda ake kara na farko da na biyu ikon yin rajistar kungiyoyin CONUA da NAMDA kuma su aiwatar da ayyuka iri daya da mai shigar da kara wato ASUU a lokaci guda.
Kanyip ya ce wannan sashin ba yana nufin karfafa kadaice iko akan kungiyoyin kwadago bane, hassali ma dai wannan sashin yana karfafa assasa wasu kungiyoyin kwadago ne.
Kotun ta sheda cewa “bukatun mai shigar da kara basu yi nasara ba, kuma ba a mince da bukatun ba sannan wannan ita ce matsayar koto.
Bisa shedun da kotu ta tabbatar, mai kara ya shigar da karar ne ta asalin sammacin da ya shigar a ranar 26 ga watan Yuni na shekarar 2022.
Dandalin Mu Tattauna