Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Ba Da Belin Abba Kyari Tsawon Makonni Biyu


Abba Kyari
Abba Kyari

Mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya bayar da belin tsohon kwamandan rundunar ‘yan sandan farin kaya DCP Abba Kyari na wucin gadi na tsawon makonni biyu bisa dalilai na alfarma da ya je ya halarcin zaman makokin mahaifiyarsa.

WASHINGTON, D. C. - An bayar da belin Kyari kan kudi Naira miliyan 50 da kuma wanda zai tsaya masa.

Da yake bayar da wannan umarni, Mai shari’a Nwite ya kuma bayyana cewa, wanda zai tsaya masa, wanda kuma shi ne lauyansa a kan lamarin, ya ajiye kwafin takardar shedar kiran sa ga mataimakin magatakardar kotun.

Kyari kuma zai ajiye fasfo dinsa na tafiya a kotu kuma ya kasance yana kai rahoto ga duk wata hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) mafi kusa da shi a cikin lokacin da aka bayar da belinsa.

Alkalin kotun ya ba da umarnin ne har sai an yanke hukuncin neman belin Kyari da aka shirya yi ranar 31 ga Mayu, 2024.

Duk da cewa Kyari ya rasa mahaifiyarsa, Yachilla Kyari, a ranar 5 ga Mayu, 2024 ne, ba a bayyana ko ya kasance wani bangare na dalilan bayar da belinsa nasa ba.

A shekarar 2021 ne, Ofishin Bincike na Tarayya ya tuhumi Kyari kan zargin damfarar Intanet na kasa da kasa da ke da alaka da Ramon Abbas, aka, Hushpuppi.

Daga baya NDLEA ta kuma kama Kyari a watan Fabrairun 2020 bisa zarginsa da aikata laifukan da suka shafi mu’amulla da muggan kwayoyi. Tuni dai aka tsare shi a gidan yarin Kuje da ke Abuja.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG