Wata kotun Amurka ta tuhumi wani dan tsohon Shugaban kasar Guinea da matarsa da zargin bautar da wata yarinya 'yar kasar ta Guinea a gidansu na alatu da ke Dalas, jahar Texas na tsawon shekaru 16.
An tuhumi Mohammed Toure da Denise Cros-Toure da laifin tilasta aikin bauta da kuma boye marar takardar izinin zama Amurka saboda amfanar kansu.
Lauyansu ya ce matsayin da gwamnati ta dauka na, ata bakinsa, "cike da kazafin assha, da kage-kage da kuma karerayi."
To amma lauyoyin da ke gabatar da kara a madadin gwamnatin Amurka sun ce iyalin na Toure sun kawo yarinyar zuwa Amurka daga kauyenta a kasar Guinea a shekarar 2000. Su ka ce shekarunta a lokaci ya kai akalla 5 idan ma bai kai 13 ba.
Makwabta ne su ka taimaka ma ta ta tsere a 2016 sannan su ka kai ta YWCA ta fake.
Ta gaya ma masu bincike cewa iyalin na Toure kan tilasta ma ta yin aiki tun daga asuba zuwa dare - ta yi ta girke-girke, da share-share, da kuma rainon yara.
Facebook Forum