Kwamitin Sulhu na majalisar dinkin Duniya yana wani taron gaggawa kan kokarin tarfa ruwa a zaman dar dar a makurdin Koriya,inda Koriya ta kudu ta kekasa kasa cewa sai tayi atisaye tareda amfani albarusai na gaske,duk da barazanar da Koriya ta Arewa tayi cewa zata mai da martani.
Rash ace ta bukaci taron na yau a New York domin aikewa da abinda ta kira “bukatar taka tsan-tsan” ga kasashen koriyoyin biyu, kuma a fara “daukan matakan difimomasiyya”,domin warware rikicin a siyasance.
Koriya Ta Kudu ta lashi takobin sai tayi wan nan atsayen a tsibirin Yeonpeong na yini daya a ranar litinin din nan ko Talata,hakan zai dogara ne kan yanayi.
Martani da Koriya Ta Arewa ta dauka a baya da Koriya ta Kudu ta yi irin wan nan atisaye ranar 23 ga watan Nuwamba shine kai wa tsibirin farmaki da makaman Egwa,ta kashe ‘yan koriya ta kudu hudu.
Koriya Ta Arewa ta kira irin wan nan mataki tsaukana,domin matakin zai sa Koriya ta kudu ta harba makamai cikin yankin ruwa da Koriya Ta Arewar take ikirarin nata ne. Ita Seoul tace irin wan nan atisayen mataki kariya ne. Arewa taceduk wani sabon atrisayen a yankin ruwan da kasashen suke gardama akai zai haifarda mummunar bala’i.
Tsohon Jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Bill Richardson, yace shawarwarin da ya yi a baya bayan nan da jami’ai a Pyongyang,ya nuna alamun “ci gaba”a kokarin warware abinda ya kira “lamari mai hadari”.
Da yake magana daga Pyongyang,Richardson, ya gayawa tashar talabijin ta CNN,cewa wani Janar na Koriya ta Arewa da ya gana da shi ba a ranar lahadin nan, ya karbi shawarar a bude layin “tarho na musamman” tsakani rundunar mayakan kasashen biyu. Yace irin wan nan layi zai taimakawa wajen tuntuba domin magana idan har wani lamari ya auku.