Jaridar New York Times ta buga labarin cewa wasu manyan hafsoshin Amurka suna bukatar fadada ayyukan sojojin Amurka na musmman zuwa yankin kabilu na Pakistan dake kusa da kan iyakar kasashen biyu.
Kamar yadda rahoton ya nuna,kwamandojin Amurka sunce amfani da sojojin na musmman wajen kamo mayakan sakan, su kai su Afghanistan domin yi musu tambayoyi,zai samar da tulin bayanai masu amfani.
Shirin bai sami amincewa ba tukun,kuma Jaridar tace wani babba jami’i a gwamnatin Obama bai goyi bayan kutse cikin Pakistan ba.Ta ambaci jami’in yana cewa a kutsen da aka yi a baya,kwalliya bata biya kudin sabulu ba,kuma bakin jinin da matakin zai haifar a Pakistan zai dara duk wani ribar da za’a samu.
Amurka tana amafani da jiragen yaki da basu da matuka wajen kaiwa mayakan sakai farmaki a yankin Kabilu na Pakistan. Jami’an Amurka basa magana kan wadan nan hare hare,illa kawai suce duka wan nan baki daya yana daga cikin shirin yaki da ‘yan ta’adda al-Qaida,wadanda suke amfani da yankin a matsayin sansani.