Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen China Da Rasha Suna Kara Matsa Lamba Kan Kasashen Koriya Ta Kudu Da Ta Arewa Su Kai Zuciya Nesa


Yankin da kasashen koriya biyu suke gardama akai.
Yankin da kasashen koriya biyu suke gardama akai.

Kasashen China da Rasha suna kara matsin lamba kan kasashen Koriyan nan biyu, kudu da arewa cewa su yi Allah su kai zuciya nesa,ganin zaman dar dar yana karuwa a makurdin.

Kasashen China da Rasha suna kara matsin lamba kan kasashen Koriyan nan biyu, kudu da arewa cewa su yi Allah su kai zuciya nesa, ganin zaman dar dar yana karuwa a makurdin.

Jiya Asabar china ta gayyaci jakadun kasashen biyu domin ta bayyana damuwarta kan shirin Koriya Ta Kudun na yin atisaye inda da albarusai daga tsibirin nan da Koriya Ta Arewa ta kai wa hari cikin watan jiya,da kuma kurarin makwabciyarta cewa martani da zata dauka zai fi tsanani kan harin da makaman Egwa da ta kai wa tsibirin muddin ta Kudun ta ci gaba da atisayin.

China ta kira hali da ake ciki a yankin mai “matukar hadari”, tace babu wani kunbiya kunbiya tana adawa kan duk wani mataki da zai kara zafafa lamarin.

Rasha ta kira taron gaggawa na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da za’a yi wani lokaci yau lahadi. Jakadan Moscow a Majalisar Dinkin Duniya,Vitaly Churkin,yace tilas kwamitin ya aikewa kaashen sako neman su yi taka tsan tsan,kuma ta taimaka wajen fara shawarwarin difilomasiyya domin warware rikicin.

Rasha ta bayyana damuwa kan atsayin da Koriya Ta Kudu zata yi da makamai na kwarai. Koriya Ta Kudu ta jingirta kaddamar da atisayen jiya Asabar saboda munin yanayi,amma wata majiyar soji tace ana sa ran aiwatar da shirin gobe litinin ko Talata,ta kara da cewa Koriya Ta Kudu tana da ‘yancin yin wan nan atisaye.

XS
SM
MD
LG