Llahadin nan, kankara da wani dan karen sanyi da ya lullube Turai ya tilas ta rufe tashoshin jiragen sama da na kasa,da hanyoyi a fadin nahiyar baki daya, wanda yasa dubban matafiya suka makale.
Tashoshin jirage a Ingila,Jamus,Faransa,da Holland da kasar Italiya duk sun bada labarin soke sauka ko tashin daruruwan jirage, ko kuma jinkiri a wasu. Tilas aka rufe hanyoyin saukar jirage a tashohin Ingila da aka fi yawan zirga zirga na Heathrow Gatwick saboda a share kankara.
Tashar jiragen sama dake Frankfurt na Jamus, ta soke tashi ko saukar jirage dari biyar yau lahadi.
Sai da aka kawo ‘yansanda a tashar jiya Asabar domin kwantar da hankulan fasinjoji dasuka fusata.
Baya tashoshin jirage da lamarin ya shafa a Ingila,hanyoyin mota da na jiragen kasa suma basu tsira a Ireland ta arewa,Wales,Scotland, da kuma Ingila.
Masana yanayi suna hasashen lamarin yana iya kara muni.