Kamfanin dillancin labarun China,Xinhua ya bada labarin cewa babban jami’in jakadancin kasar China Dai Bingguo, ya shaidawa shugaba Lee Myung-bak na Korea ta kudu cewa China zata ci gaba da kokarin daukan matakan rage zaman dar-dar da ake yi ta hanyar shirya tattaunawa a tsakanin Korea ta kudu da Korea ta Arewa. Jakadan na kasar China ya furta hakan ne a ziyarar day a kai Seoul, babban birnin kasar Korea ta kudu a dai dai lokacin da ake shirin hadin gwiwar rawar dajin rundunar sojin ruwan Amirka da ta Korea ta Kudu.A dai dai lokacin da China ke kokarin shirya sulhu tsakanin Korea ta Kudu da Korea ta Arewa, jami’an Gwamnatin Korea ta Kudu sun bada rahoton cewa anji karar harbe-harben makamai masu linzami daga shiyyar Korea ta Arewa dake yiwa tsibirin kan iyakar Korea ta kudu barazana.
Wani babban jami’in Jakadancin Kasar China, ya shaidawa shugaba Lee Myung-bak na Korea ta kudu cewar China zata ci gaba dakokarta ganin an kai ga rage zaman tankiya tsakanin Korea ta Kudu daKorea ta Arewa.