WASHINGTON DC —
Direktar dake kula da harkokin da suka danganci Amurka a ma’aikatar harkokin wajen kasar Korea ta arewa Choa Son Hui ta fada a yau Asabar cewa a shirya kasar sa take tayi shawarwari da Amurka, a yanayi ko kuma ka’idodin da suka dace.
Ms Choa Son Hui tayi wa yan jarida wannan furuci a filin saukar jiragen sama bayan ta koma gida daga ziyarar data kai kasar Norway.
Har yanzu jami’an gwamnati Amurka basu maida martini ga wannan furuci da direktar tayi ba.
Facebook Forum