Wannan na daga cikin batutuwan da suka dauki hankulan mahalarta zaman jin ba’asin jama’a kan kudirin dokar da zata tilasta masu niyyar aure gwajin kwayar cutar sida da kwamitin kula da lafiya na majalisar dokokin jihar Adamawa ya shirya lokacin.
Shugabar kungiyar Malama Farah James ce ta dago batun ganin dokar zata sa a samu karuwar mabukata maganin da a yanzu haka ya yi karanci a daidai lokacin da ake neman janye tallafin.
Shima babban sakataren cibiyar kula da masu dauke da kwayar cutar sida na jihar Adamawa Dr, Stephen John ya shaidawa kwamitin cewa an sami karuwar masu dauke da kwayar cutar daga kashi daya da digo tara zuwa kashi biyu da digo biyar wanda ya danganta da ayukan ta’addancin na Boko Haram da ya raba masu fama da cutar da wuraren da suke karbar magani da kuma janye tallafin a makwabciyarta ta jihar Taraba da aka yi.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar Adamawa Dr, Fatima Atiku Abubakar ta ce janye tallafin ba zai zama barazana ga kokarin da ake yi na yaki da cutar ba saboda a cewarta akwai tsari na gwamnatocin tarayya da jihohin na cire wani kaso daga kudin da suke samu daga asusun tarayya don sayan maganin kai tsaye saboda hana jihohi karkata kudade idan ta sakar masu mara.
Amincewar majalisar dokoki da bangaren zartaswa inji kakakin majalisar dokokin jihar Adamawa Hon. Kabiru Mijinyawa zai sa a yi hukunci mai tsanani ga masu shirin yin aure da suka keta ta ko ga daya daga cikinsu da ke da kwayar cutar amma ya nemi boyewa. Idan hakan ya faru ana iya hana daurin auren idan sun ki yin gwajin.
Kudirin dokar gwajin kwayar cutar sida mako daya kamin daurin auren ya samu karbuwa ga mabiya addinan Kirista da Musulumci, kungiyoyi masu zaman kansu da masu ruwa da tsaki a harkar kiwon lafiya a yayin zaman jin ba’asin jama’ar kamar yadda yake kunshe a kasidu da suka gabatarwa Kwamitin.
Saurari Karin bayanin rahoton Sanusi Adamu.
Facebook Forum