Fatan da kasar China ke yi na farfadowar tattalin arzikinta cikin sauri bayan barkewar cutar COVID-19 ya tsaya cik, yayin da annobar da ta addabi duniya ke daukar sabon salon shafar masana’antun dake fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje.
Soke odar kayayyaki da masu sayayya suka yi daga kasashen yammacin duniya ya tilastawa kamfanonin China da dama ci gaba da kasancewa a rufe, sai dai wasu daga cikinsu sun sauya zuwa samar da kayayyakin kiwon lafiya kamar ababen rufe hanci.
Masharhanta sun ce hakan na iya haifar da ci gaba da rufe masana’antu a nan gaba da kuma haddasa karancin ayyukan yi, lamarin da zai sa kusan adadin wadanda suka kammala karatun jami’a miliyan tara, zasu shiga fafutikar neman aiki a kasar China a wannan bazarar.
Facebook Forum