Annobar coronavirus na iya sa Birtaniya ta yi watsi da wata yarjejeniya, wadda dama ke cike da takaddama, wadda ta cimma da babban kamfanin fasahar sadarwar nan na China, Huawei.
Abin da jami’ai suka ce martani ne, kan yada bayanan karya da China ta ke yi game da asalin inda cutar Covid-19 ta fito, da kuma rashin bayar da bayanan gaskiya kan girman illar cutar.
Jami’an Birtaniya sun ce kamata ya yi China ta fuskanci tuhuma kan cutar Coronavirus, wadda tun farko ta bullo daga birnin Wuhan na kasar China a karshen shekarar da ta gabata.
Yayin da yawan mutanen da suka mutu sanadiyar cutar ke karuwa a Birtaniya, ministoci da yawa na kira ga frai minista Boris Johnson da ya sauya shawararsa ta barin kamfanin China na Huawei ya gina wani bangare na sabuwar fasahar 5G a Birtaniya, wanda dama Amurka ta yi ta kokarin ganin an hana saboda tsaro, tun ma kafin wannan cuta ta bayyana.
Facebook Forum