Mataimakin jagoran kwamitin shugaban kasa kan farfado da shiyyar Arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Tijjani Musa Tumsah, ya ce cikin shirin gwamnatin tarayya mai suna ‘Buhari Plan’ ana so a mayar da hankali ne kan kiwon lafiya a matakin farko.
Haka kuma shirin na yin kokarin isar da kiwon lafiya ga yankunan da basu da halin zuwa ganin likita ko sayen magani, domin mutane su sameshi kyauta kuma a kofar gidajensu.
Yanzu haka dai ‘yan kwamitin sun zagaya dukkan jihohin yankin shida, inda mutane fiye da dubu 25 zuwa 30 suka sami cin moriyar wannan shiri, wanda ya hada da aikin ido da tiyatar jiki da dai sauransu.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Hassan Maina Kaina.
Facebook Forum