Kungiyar matasa ta kabilar Ron-Kulere a jihar Filato ta ba da shawarar a taimakawa Fulani makiyaya ta yadda za su kebe dabbobinsu a abin da suka kira "shinge" maimakon yawon da suke yi, lamarin da suke gani zai kawo karshen fito-na-fito da makiyaya da manoma ke yi a wurare da dama.
A wani taron manema labarai da suka kira, mai magana da yawun kungiyar Machan Makut, ya ce idan gwamnati za ta tallafawa makiyaya su kebe shanunsu a "shinge" kamar yada masu kiwon kaji, awaki da aladu ke yi zai taimaka wajen rage tashin hankalin da ake samu a sassa kasar.
Amma daya daga cikin shugabannin kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Filato, Nura Muhammad ya ce idan an ce "shinge" wuri ne dan kankani da ba zai isa shanu su yi kiwo ba.
Amma shinge babba wanda a turance ake kira ranch inda za'a debi katafaren fili a shuka ci yawa a ba Fulani su yi kiwo shi ne zai zama samar da maslaha, inji Nura Muhammad.
A cewar Nura, ya taba ba gwamnatin tarayya shawara kan yadda za a gyarawa makiyaya dajin Birnin Gwari da na Sambisa.
Amma Farfesa Yusuf Turaki wanda yake ganin matsalar ta fi kamari ne a jihohin da ke tsakiyar Najeriya, ya nuna gazawar gwamnatin wajen samar da cikakken tsaro ga mazauna karkara, lamarin da ya ce ya kan tilastawa mutane tashi tsaye domin kare kansu.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.
Facebook Forum