Attoni-Janar din Shari’ar Amurka ya ba da umurnin a gaggauta yin nazarin yadda Ma’aikatar Shari’a da kuma Hukumar Bincike ta FBI kan dau mataki game da mutanen da ake ganin wata rana za su iya kashe mutane da dama.
Wannan ya biyo bayan amsa kuskurenta, a jiya Jumma’a, da hukumar bincike ta FBI ta yi, wadda ita ce babbar hukumar tabbatar da bin doka da oda - wadda ta amsa cewa ta yi sakaci ba ta bi diddigin bayanan da aka ba ta ba game da dan bindigar nan wanda ya hallaka mutane 17 ya kuma raunata wasu 14 a wata makaranta a jahar Florida ranar Laraba.
Jiya Jumma’a Hukumar binciken ta FBI ta amsa cewa ba ta bi tsarin da aka saba bi ba bayan da aka ba ta bayani tuntuni, game da maharin mai suna Nikolas Cruz. Hukumar ta FBI ta ce wani na kusa da Cruz ya rada ma ta ranar 5 ga watan Janairu game da sha’awar matashin ta kashe mutane da kuma wasu bayanai masu tayar da hankali.
Facebook Forum